IQNA

Ana Shirin Gudanar Da Wata gasar Kur’ani ta Yanar Gizo A Kasar Bahrain

22:42 - September 01, 2012
Lambar Labari: 2402813
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wata gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a kasar Bahrain ta hanyar sadarwa ta yanar gizo a wani mataki na karfafa lamarin kur’ani da mabiya tafarkin iyalan gidan manzo suke a tsakanin al’ummar kasar wadda aka shagaltar da ita da wasanni da rafkana daga bin Allah.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga safin sadarwa na yanar gizo na Laha online, cewa yanzu haka ana shirin gudanar da wata gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a kasar Bahrain ta hanyar sadarwa ta yanar gizo a wani mataki na karfafa lamarin kur’ani da mabiya tafarkin iyalan gidan manzo suke a tsakanin al’ummar kasar wadda aka shagaltar da ita da wasanni da rafkana daga bin Allah madaukakin sarki.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
Masana da dama suka ganin a lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mutane da ba musulmi ba.
1088356


captcha