Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo n businessnews, cewa ana shirin fara gudanar da wani shiri na horar da malaman addinin muslunci da kuma limaman masallatai a aksar Tunisia domin shiga yaki da tsauran ra’ayin addini wanda ya zama ummul haba’isin da dama daga cikin matsalolin da ake fama da su a duniyar musulmi ta yau, kamar yadda ake gani a cikin kasashe irin Tunisia da Libya.
Jam’yyun adawa da kungiyoyin farar hula a kasar Bahrain sun yi kira zuwa ga gudanar da wani babban gangami a yau a birnin Manama fadar mulkin kasar, domin yin kira ga mahukuntan kasar da su saki fursunonin siyasa da suke tsare da su.
A cikin wani bayani na hadin gwiwa da jamiyyun gami da kungiyoyin suka fitar, sun bayyana cewa mahukuntan kasar Bahrain suna ci gaba da tsare dubban mutane da suka hada da jagororin jamiyyun siyasa masu adawa, da kuma shugabannin kungiyoyin kare hakkin bil adam saboda ra’ayoyinsu na siyasa, wanda hakan ya yi hannun riga da dukaknin dokokin kasa da kasa.
A ranar juma’ar da ta gabata ma an gudanar da wata gagarumar anga-zangar a dukaknin fadin kasar ta Bahrain domin nuna rashin amincewa da salon mulkin mulukiya na kasar wanda Amurka da Birtaniya suka kafa sama da shekaru 100 da suka gabata, tare da taimakon gidan sarautar Ali-Saud da ke mulki a Saudiyya.
1089425