IQNA

An jadda Wajabcin Mayare Da hankali kan Makircin da Makiya Suke Shirma Larabawa Da Musulmi

17:58 - September 04, 2012
Lambar Labari: 2405155
Bnagaren kasa da kasa, an yi kira ga dukaknin musulmi da larabawa da su zama cikin fadaka kan makircin da ake shirya musu wanda manyan kasashen duniya masu giman kai ne suke kan gaba wajen shiya shi da nufin bayar da kariya tasiyasa da tsaro ga haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa masan ada dama sun yi amnar cewa, an yi kira ga dukaknin musulmi da larabawa da su zama cikin fadaka kan makircin da ake shirya musu wanda manyan kasashen duniya masu giman kai ne suke kan gaba wajen shiya shi da nufin bayar da kariya tasiyasa da tsaro ga haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya kamr dai yadda bayanin ya tabbatar.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa makiya al’ummomin musulmi da larabawa suna kokarin haifar da fitinu domin mantar da su batun palastinu da masallacin Qods, domin hakan ya baiwa Isra’ila damar cin karenta babu babbaka.
Sayyid Nasrullah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa tare da shugaban tashar talabijin ta Al-mayadeen Gassan Bin Juddu, inda ya sheda cewa makiyan al’ummar musulmi da larabawa su ne suke da hannu kai tsaye wajen haifar da dukkanin rikice-rikicen da ake yi a cikin kasashne musulmi, babbar manufar hakan kuma ita shagaltarsu daga batun Palastinu da kuma halin da masallacin Qods yake ciki, wanda a halin yanzu suke son rusa shi.
Dangane da batun rikicin Syria kuwa, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa Amurka da Isra’ila su ne suke tafiyar da rikicin tare da taimakon gwamnatocin larabawa da suke yi musu hidima, ya ce tun farkon rikcin ya zanta da shugaba Assad, kuma ya tabbatar da aiwatar da dukaknin sauye-sauye da ‘yan adawa suke bukata, amma kuma suka ki amincewa da duk wani batun sulhu da fahimtar juna, maimakon haka ma sai kasashen yamma da kawayensu daga cikin larabawa suka bas u tarin makamai da kudade domin su shelant ayaki kan gwamnatin Syria.

1090119
captcha