Bangaren kasa da kasa, bababr cibiyar mabiya addinin muslunci a kasar faransa ta shirya gudanar da wani zaman taro domin wayar da kan masu niyyar zuwa aikin hajji bana daga kasar domin sanin abin da za su idan sun isa kasa mai tsarki wanda hakan ke tabbatar da cewa lokacin yana ci gaba da karatowa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin saarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, bababr cibiyar mabiya addinin muslunci a kasar faransa ta shirya gudanar da wani zaman taro domin wayar da kan masu niyyar zuwa aikin hajji bana daga kasar domin sanin abin da za su idan sun isa kasa mai tsarki wanda hakan ke tabbatar da cewa lokacin yana ci gaba da karatowa domin gudanar da wannan babbar ibada.
Kasar Afrika ta kudu ta ce; muhimmin abinda ta sa a gaba shi ne taimakawa nahiyar Afrika ta ci gaba da kuma kokarin an sami tabbataccen zaman lafiya a cikinta, a wani bayani da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a jiya juma'a ta bayyana cewa; A shekarar kudi da ta gabata, kasar ta maida hankali ne wajen taimakawa kasashen Afrika daban-daban domin cimma wannan manufa.
Har ila yau, bayanin na ma'aikatar harkokin wajen Afirka ta kudun ya ce; kasar ta bada kudade ga hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa domin gudanar da ayyuka da kuma gwaje-gwaje a cikin wasu kasashen nahiyar Afrika saboda yin fada da cutuka masu yaduwa.
Wani sashe na bayanin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya ce: Gwamnati ta kashe kudaden da su ka kai Rand miliyan 126 wajen taimakawa kasashen kungiyar "Sadak" da kayan abinci. Haka nan kuma kasar ta baiwa kasar cuba taimakon kudin da su ka kai Rand miliyan 100.
1095352