IQNA

Imam Sadiq (AS) Yana Da Matsayi Na Musamman A Wajen Ahlu Sunna

22:51 - September 12, 2012
Lambar Labari: 2410344
Bangaren kasa da kasa, Imam Jafar Sadiq ba daya ne kawai daga cikin limaman ahlul baiti ba shi ya kasance malami na dukkanin musulmi sunna da shi’a domin shi ne wanda ya raya ilimi da dukkanin al’ummar musulmi suke amfana da shi a dukkanin mazhabobi ko da kuwa an samu banbanci da yadda shi ya koyar.
Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin malaman jami’oin Pakistan ya bayyana cewa Imam Jafar Sadiq ba daya ne kawai daga cikin limaman ahlul baiti ba shi ya kasance malami na dukkanin musulmi sunna da shi’a domin shi ne wanda ya raya ilimi da dukkanin al’ummar musulmi suke amfana da shi a dukkanin mazhabobi ko da kuwa an samu banbanci da yadda shi ya koyar amma dai shi ne tushe.
A bangare guda kuma wani bayanin ya ce gwamnatin Syria ta aike da wasu wasiku biyu zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya da kuma shugaban kwamitin tsaron majalisar, dangane da karuwar ayyukan ta'addanci bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
A cikin wasikun biyu, gwamnatin Syria ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta safke nauyin da ya rataya a kanta, wajen matsa lamba kan gwamnatocin da suke taimaka ma ayyukan ta'addanci a cikin kasar Syria, ta hanyar baiwa 'yan bindiga makamai da makudan kudade, domin kuwa a cewar bayanin, idan har gwamnatin Syria za ta amince da wannan yarjejeniya da kuma yin aiki da ita, babu dalilin da zai sanya a bar daya bangaren rikicin yana cin karensa babu babbaka.
Bayanin ya ce tawagogi na masu sanya ido na kasashen larabnawa da majalisar dinkin duniya sun gane wa idanunsu hakikanin abin da ke faruwa a kasar, saboda haka kawo karshen tashin hankali a kasar ya doru ne kan dakatar da kasashen masu taimaka ma ayyukan ta'addanci, musamman ma na larabawa daga cikinsu, wadanda suka sanar da hakan a hukumance.
1096401


captcha