IQNA

Misrawa Sun Bukaci Gwamnatin kasarsu Ta Yanke Duk Wata Hulda Da Kasar Amurka

22:30 - September 14, 2012
Lambar Labari: 2411146
Bangaren kasa da kasa, dubban misrawa da suka gudanar da zanga-zanga a jiya a birnin Alkahira sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta dauki matakin yanke duk wata alaka da gwamnatin Amurka sakamakon cin zarafin addini da ake yia kasar da sunan yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa nayanar gizo na tashar Al-ala, cewa dubban misrawa da suka gudanar da zanga-zanga a jiya a birnin Alkahira sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta dauki matakin yanke duk wata alaka da gwamnatin Amurka sakamakon cin zarafin addini da ake yia kasar da sunan yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi amma a kan msulunci kawai.
marubucin kasar Masar Ala Aswani ya ce mika mulkin kasar Masar ga hannun Ahmad shafiq tsohon pita ministan kasar lokacin mulkin tsohon shugaban mulkin kama karya Husni Mubarak hakan na nufin cewa juyin juya halin da al’ummar kasar suka yi ya kawo karseh kenan domin wadanda aka kawar sun dawo.
mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.
Tafiyar da Ali Juma’a ya yi zuwa birnin Qods ya yi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta haramatcciyar kasar Isra’ila wanda kuma ko shakka babu hakan ya sanya gagarumin shakku a cikin zukatan mutanen kasar dangane da wannan ziyara tasa, duk kuwa da cewa daga cikin abubuwan da ya yi har da duba lafiyarsa a asibiti. 1097406
captcha