IQNA

Jmai’an Tsaron Gwamnatin Saudiyya Sun Rusa Wani Masallaci A Gabacin Kasar

23:17 - September 17, 2012
Lambar Labari: 2413785
Bangaren kasa da kasa, jamia’n tsaron kasar aSaudiyya sun kai farmaki kan wani masallaci na mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a wani mataki na kara tsananta gabarsu kan duk wani mabiyin tafarkin manzon Allah da ke yankin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habrta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo natashar talabijin din Al-alam, cewa jamia’n tsaron kasar aSaudiyya sun kai farmaki kan wani masallaci na mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a wani mataki na kara tsananta gabarsu kan duk wani mabiyin tafarkin manzon Allah da ke yankin na gabacin kasar.
sabuwar dokar da aka kafa a kasar Saudiyya dangane da wajabta ma mutane dakatar dukkanin ayyukansu a lokacin salla a kasar Saudiyya hakan ya jawo rikici a tsakanin mutanen kasar da kuma mahukunta, sakamakon matakan da gungun mutanen da ake kira masu hani daga mummna da umurni da kyakkayawa suke aikatawa da sunan suka kare addini tare da izini daga masarautar wahbaiyawan kasar.
A lokacin da malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mabiya addinai kamar majamioin mabiya addinin kirista.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
Masana da dama suka ganin a lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mutane da ba musulmi ba.
1099146













captcha