IQNA

Fim Din Cin Zarafin Manzo Ya Fi Littafin Ayoyoyin Shaidan Muni

17:39 - September 18, 2012
Lambar Labari: 2414557
Bnagaren kasa da kasa, bababn sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa fitar da littafin ayoyin shaidan da aka ayi a wasu shekaru da suka gabata yan ada muni amma fim din da Amurkawa suka fitar a cikin lokutan nan ya fi muni.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-manar, cewa bababn sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa fitar da littafin ayoyin shaidan da aka ayi a wasu shekaru da suka gabata yan ada muni amma fim din da Amurkawa suka fitar a cikin lokutan nan ya fi muni idan aka kwatanta abbubuwan ad suke ciki.
A nasu bangare yan majalisar ta bukaci ficewar sojojin ne bayan sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayar da ke cewa ta aike da sojojinta zuwa birnin na Sanaa domin bayar da kariya ga ofishin jakadancinta a can, biyo bayan zanga zangar da mutanen birnin suka yi a harabar ofishin a jiya jumma’a. inda suke nuna fushinsu kan majigin nan na batunci ga manzon Allah.

Yansanda a kasar ta yemen dai sun kama mutane da dama sun tsare kan zanga zangar nuna fushin da suka yi kan batanci ga Musulunci.

Har’ila yau an gudanar da zanga zangar nuna fushi ga majigi mai batunci ga Musulunci a birnin Sudney na kasar Australia a gaban ofishin jakadancin kasar Amurca, Yan sandan gwamnatin Australia sun kama mutane da dama, wasu kuma sun samu raunuka a lokacin da yansanda suke kokarin tarwatsa su.

A nata bangaren majalisar dokokin kasar Afganistan ta yi Allah wadai da majigin wanda yake muzanta manzon Allah (s), kuma ta bukaci kasar Amurka ta haramta majaigin ta kuma gurfanar da wadanda suke da hannun wajen yin sa, kamar yadda majaliar ta bukaci da a janye dukaknin yarjeniyoyin tsaro da aka rattaba hannu kansu tsakanin Amurka da Afhanistan.

Tun bayan fitar da wannan fim na batunci ga manzon Allah da Amurkawa suka yi, al'ummomin musulmi na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a koina cikin fadin duniya, domin tabbatar wa Amurka cewa dukaknin jsulmi sun yi imanin cewa manzon Allah yana birbishinsu, kuma yin batunci a gare shi wuce dukkanin iyakoki ne a addinin muslunci.

1100003















captcha