IQNA

Dubban Turkawa Cikin Fushi Sun Kone Tutar Amurka A Birnin Ankara

17:38 - September 18, 2012
Lambar Labari: 2414563
Bangaren kasa da kasa, dubban Turakawa sun gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da gwamnatin Amurka danagane da cin zarafin da Amurkawa suka yi wa addini tare da goyon bayan gwamnatin kasar bisa hujjar yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra'ayi wanda hakan ya yi hannaun riga da dukaknin dokoki na kasa da kasa.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar ta kasar Lebanon, cewa dubban Turakawa sun gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da gwamnatin Amurka danagane da cin zarafin da Amurkawa suka yi wa addini tare da goyon bayan gwamnatin kasar bisa hujjar yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra'ayi wanda hakan ya yi hannaun riga da dukaknin dokoki na kasa da kasa kamar yadda masana suka tabbatar da hakan.

Ministan harkokin waje kasar Aljeriya ya bayyana cewar suna ci gaba da kokarin gano gaskiyar labarin kashe jami'in jakadancin Aljeriya da ke hannun 'yan tawayen Mali da suke rike da yankunan arewacin kasar.
Murad Madlisi ministan harkokin wajen kasar Aljeriya a yau litinin ya bayyana cewar tun bayan watsa labarin cewa 'yan tawayen Mali masu tsaurin ra'ayin Islama da suke rike da yankunan arewacin kasar sun kashe jami'in diflomasiyyar kasar Aljeriya da suka yi garkuwa da shi, har ya zuwa yanzu gwamnatin Aljeriya ba ta samu tabbacin labarin ba, amma tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Har ila yau kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Aljeriya a jiya lahadi ya sanar da cewa; Mahukuntan Aljeriya suna ci gaba da gudanar da bincike kan gaskiyar labarin da aka watsa na kashe jami'in diflomasiyyar Aljeriya a kasar Mali.
Gidan talabijin din Aljezeera mallakin kasar Qatar ce ta watsa labarin cewa; 'Yan tawayen Mali da suka mamaye yankunan arewacin kasar sun kashe jami'in diflomasiyyar Aljeriya da suka yi garkuwa da shi. 1100145
captcha