Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa malaman addinin muslunci a garin Sur sun karba kiran kare martabar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka kamar dai yadda babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah ya yi kira da a gudanar da jerin gwano a garin.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya ja kunnen gwamnatin Amurka dangane da abin da zai biyo baya matukar dai ta bari aka watsa dukkanin fim din nan na cin mutumcin Musulunci da Manzon Allah (s.a.w.a) da aka shirya a Amurkan.
Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne dazu-dazun nan a jawabin da ya gabatar a wajen jerin gwanon nuna rashin amincewa da cin mutumcin Manzon Allah (s.a.w.a) da kungiyar Hizbullah din ta shirya a birnin Beirut babban birnin kasar Labanon din inda ya ce wajibi ne Amurka ta fahimci cewa watsa cikakken wannan fim na cin mutumci lamari ne da ke haifar mata da mummunan sakamako don haka wajibi ne ta hana yada shi.
Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa wannan fushi da suka nuna a yau ba wani lamari ne da zai wuce haka nan kawai ba, yana mai cewa ya kamata makiya su san cewa cin mutumcin Manzon Allah (a.s) abu ne da ba za a taba amincewa da shi ba sannan kuma fitowar da suka yi a yau mafari ne na wannan fushi na su har sai an cimma manufa.
Sayyid Nasrallah ya kirayi al’ummar musulmi da su kaurace wa shafuffukan internet da suka yada wannan fim din yana mai cewa gazawar al’ummar musulmi wajen aikata wani abu a wannan bangaren nuna gazawa ne ga hakkin Manzon allah (s.a.w.a).
1101060