Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a nahiyar Afirka, cewa dubban musulmi sun gudanar da jerin gwano a tarayyar Nigeria domin nuna rashin amincewa da kuma yin kakkausar suka kan fim din nan na batunci da aka fitar da ke tozarta manzon rahma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da Amurkawa suka yi.
A garin Kaduna na tarayyar Najeriya, a yau litinin dubun dubatar musulmi ne suka gudanar da zanga-zangar lumanar nuna fushinsu a game da fim din nan na cin zarafin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah da iyalan gidansa tsarkaka da aka shirya a kan manufa a kasar Amurka. Zanga-zangar wacce ta gudana a cikin tsanaki, a lokacin gudanar da ita mutanen na dauke da manyan alluna da kuma kyallaye wadanda a kansu musulmin ke nuna rashin amincewarsu da wannan fim, yayin da a kan sauran allunan aka rubuta kalaman tsinuwa akan Amurka, Birtaniya da kuma Haramtacciyar kasar Isra'ila.
Daga bisani dai masu zanga-zangar sun tsoma tutocin wadannan kasashe 3 a cikin turbaya, sannan kuma jama'a suka rika tattaka su kafin kuma sun cinna masu wuta. Daya daga cikin shuwagabannin kungiyoyin kare hakkokin bil'adama da ke yankin mai suna Malam Shehu Sani da ya halarci zanga-zangar, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa cewa, da shi da sauran jama'ar da suka fito a yau, sun yi hakan ne domin nuna rashin amincewarsu da duk wani abu da zai taba matsayi da kimar manzon Allah mai tsira da amincin Allah da alayensa kamar dai wannan fim da aka shirya a Amurka.
1106045