Bnagaren kasa da kasa, mahukuntan gwamnatin wahabiyawan saudiyya na ci gaba da yin amfani da karfi domin murkushe fararen hula masu neman sauyi a cikin harkokin siyasa na kasar sakamakon zalinci da danniyar da suke fuskanta daga mahukuntan kasar da suka zama bayi ga Amurka da turawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa mahukuntan gwamnatin wahabiyawan saudiyya na ci gaba da yin amfani da karfi domin murkushe fararen hula masu neman sauyi a cikin harkokin siyasa na kasar sakamakon zalinci da danniyar da suke fuskanta daga mahukuntan kasar da suka zama bayi ga Amurka da turawa da ma yahudawan sahyuniya.
An gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta Masar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban taro ya kayatar matuka, bisa la’akari da cewa kasar Masar tana da matukar muhimamnci a cikin kasashen larabawa da kuma yankin nahiyar Afirka baki daya, wannane ma ya sanya yanzu haka kasashen larabawa da suke yin amshin shata ga siyasar turawa.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, dubban daruruwan mutanen ne suka gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta masar mai dogon tarihi.
1108702