Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa masu neman sauyi a kasar Bahrain suna goyon bayan masu neman sauyi ta hanyar lumana a kasar Saudiyya da suke neamn a samu gwamnati wadda mutane za su zaba da kansu maimakon zama bayin sarki mallakarsa.
Miliyoyin mutane sun gudanar da zanga-zanga adukkanin biranan jamhuriyar muslunci ta Iran da suka hada da birnin Tehran fadar mulkin domin nuna rashin amincewa da makircin Amurka na hada kasar Bahrain da kuma kasar saudiyya bayan da suka kasa murkushe yunkurin neman sauyi da al’ummar kasar ke yi ta hanyar lumana sama da shekara guda.
Masu neman sauyi a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da taron da shugabannin kasashen larabawa suka gudanar a kasar Iraki saboda yadda zaman taron ya kawar da idonsa kan abin da yake faruwa a kasar na cin zarafin fararen hula masu zanga-zangar lumana a fadin kasar ta Bahrain.
Gungun 14 ga watan Fabrairu da ke jagorantar boren neman sauyi a Bahrain, wanda dukkanin bangarori na kasa da kasa suka tabbatar da cewa sama da kashi tamanin cikin dari ne suke gudanar da wannan bore, gungun ya fitar da wani bayani da ya yi kakakusar suka a cikinsa, dangane da yadda wadannan kasashen suke nuna banbanci tsakanin al’ummomin larabawa.
Masu neman sauyi a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da taron da shugabannin kasashen larabawa suka gudanar a kasar Iraki saboda yadda zaman taron ya kawar da idonsa kan abin da yake faruwa a kasar na cin zarafin fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman hakkokinsu da aka haramta musu.
1110916