IQNA

Kungiyoyi na Ci Gaba Da Yin Allah Wadai Kan HKI

15:46 - October 29, 2012
Lambar Labari: 2439943
Majalisar Dokokin Kasashen Larabawa ta yi Allah wadai da hare haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna kai kan cibiyar kera makaman kasar Sudan.
Majalisar Dokokin Kasashen Larabawa a yau Lahadi ta yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da hare haren da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan cibiyar kera makaman Sudan na Yarmuk da ke kudancin birnin Khartum fadar mulkin kasar, tare da bayyana hare haren da cewar kokari ne na neman raunana karfin Sudan a fuskar kare tsaron kasarta.
Shugaban Majalisar Dokokin Kasashen Larabawa Ali Salim Dikaba'si ya bayyana cewar wannan shi ne karo na uku da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai hare haren wuce gona da iri kan Sudan da nufin karya karfinta a fuskar ci gaban da take samu na kare tsaron kasarta.
Dikaba'si ya kara da cewar hare haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan cibiyar kera makaman kasar Sudan aikin ta'addanci ne mai hatsarin gaske da ya keta dokokin kasa da kasa,
1127569
captcha