Majiyar asibiti daga yankin Rimal na birnin Gaza ta bayyanawa AFP cewa harin da jiragen yakin HKI suka kai kan ginin gidan Television na Al-Quds ya jawo raunata yan jaridu 6 wadanda suke karban magani, sannan daya daga cikinsu ya rasa kafarsa a harin.
Ashraf Al-qudra wani jami'an ma'aikatar lafiya a yankin na Gaza ya fadawa AFP cewa jiragen yakin yahudawan sun kai hari kan gidan television na al-qudas tv wanda ya sanya dukkan yan jaridu suka fice daga cikin ginin kafin hare haren da suka biyu baya a kan ginin.
Har'ila yau akwai rahotannin da suka bayyana cewa an cilla makama kan sojojin yahudawan da ke mamaye da tuddan Golan na kasar Syria a safiyar yau lahadi daga cikin kasar Syria, amma babu rahoton ko akwai wanda makamin ya fada kansa. HKi ta kwace tuddan Jolan ne tun yakin shekara ta 1967.
1138505