Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cew, Ayatollah Isa Kasim babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain yay i kakakusar suka dangene da kisan da mahukuntan kasar suke yi kan fararen hula masu zanga-zangar lumana neman sauyi da hakkokinsu da aka danne musu a matsayinsu na ‘yan kasa masu cikakken hakki.
Mutanen biyu ne suka kai ga shahada a zagaye na farko na jerin gwanon lumana wanda mutanen kasar Bahrain suka fara a yau don cika shekaru biyu da fara juyin juya halin akasar. Wani matashi mai suna Hussain Al-jazaeri, da kuma wata yarinya mai suna Aminatu Mahdi duk sun rasa rayukansu ne sanadiyyar shakar hayaki mai sa hawaye wanda jami'an tsaron kasashen Bahrai da na saudia suka cilla kan gidajensu.
Har'ila yau jami'an tsaron na kasar Bahrain sun ci gaba da jefa hayaki mai sa hawaye a unguwannin daban daban a garuruwa daban daban na kasar ta Bahrain a yau Alhamis. Banda wannan wata majiya ta bayyana cewa gwamnatin kasar Bahrain ta rufe wani sashe na filin sauka da tashin jiragen sama na binin Manama a yau din.
Wasu kafafen yada labarain sun bayyana cewa jami'an tsaron kasar Bahrain din sun kama wakilin kamfanin dillancin labarai na Associated Press Mohammad Al-Sheikh, da Hassan Jamal na kamfanin AFP na kasar Fransa sai kuma Mazin Mahdi na kamfanin dillancin labaran DPA na kasar Jamus.
1188991