Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin masu adawa da gwamnatin Morsi a kasar Masar suna da kykayawar dangataka da kasashen ketare kamar yadda aka samu wasu bayan da ke tababtar da sace wasu kayayyakin tarhin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wasu daga cikin masu adawa da gwamnatin Morsi a kasar Masar suna da kykayawar dangataka da kasashen ketare kamar yadda aka samu wasu bayan da ke tababtar da sace wasu kayayyakin tarhin kasar zuwa wasu yankuna na daban.
Wata jaridar kasar Amurka ta watsa labarin cewa: Sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya yi alkawarin tallafawa 'yan adawan kasar Masar da miliyoyin kudade, shafin Internet na Al-Misriyun a yau Laraba ya nakalto daga jaridar kasar Amurka ta McClatchy da ke da cibiya a jihar Californiya ta kasar Amurka cewa: A yayin ziyarar aikin baya bayan nan da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya kai zuwa kasar Masar ya yi alkawarin gabatar da tallafin kudade dalar Amurka miliyan 60 ga 'yan adawan kasar ta Masar.
Shafin na Al-Misriyun ya kara da cewa; A ziyarar aikin da John Kerry ya kai zuwa Masar a makon da ya gabata ya gana da shugabannin jam'iyyun adawar kasar musamman jam'iyyun adawa shida da suka yi fice a fagen kiyayya da gwamnatin Muhammad Morsi.
1203854