Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, yanakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Wasu majiyoyin tsaron kasar Birtaniya sun sheda cewa, sakamakon binciken da aka gudanar kan da aka yi wa wani sojan kasar a jiya Larabawa a birnin London ya nuna cewa, mutanen da ake tuuma da laifin 'yan kasar Birtaniya ne amma 'yan asalin Najeriya.
Wasu daga cikin kafofin yada labaran kasar Birtaniya sun bayyana cewa, daya daga cikin wadanda ake tuhuma mai suna Mikel Adebolajo dan shekaru 28 da haihuwa, an haife shi ne a kasar ta Birtaniya, kuma mazaunin birnin Landan ne amma dan asalin Najeriya, kuma ana sa ran dukkanin bmutanen biyu an haife su ne a cikin addinin kiristanci, daga baya kuma suka karbi addinin musulunci.
Yanzu haka dai dukkanin mutanen biyu suna tsare a asibiti inda ake yi musu magani, sakamakon harbinsu da 'yan sanda suka yi da bindiga, a cikin shekara ta 2005 an kai wani hari a cikin wata unguwa da ke cikin birnin Landan, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10, wanda shi ma aka zargi musulmi da aka ce masu tsattsauran ra'ayi ne.
1234710