Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron, Jagoran ya isar da sakon taya murnarsa ga al'ummar musulmi dangane da wannan rana mai albarka ta haihuwar Imam Husaini (a.s). Jagoran ya bayyana cewar: Imam Husain (a.s) ya sadaukar da ransa da na masoyansa da kuma kama iyalansa da Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) a matsayin fursunoni don ci gaba da wanzuwar Musulunci da kuma kyamar zalunci, sannan kuma ya gabatar da hakan ga dukkanin bil'adama a matsayin abin koyi.
Jagoran ya bayyana cewar dukkanin rayuwar Imam Husain (a.s) cike take da darasi da kuma abin koyi sai dai waki'ar Karbala, saboda irin girma da daukakar da take da ita ne tafi yin fice da kuma mamaye sauran abubuwan da suka faru a rayuwar Imam Husain din.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mafi muhimmancin darasin da ke cikin yunkurin Imam Husain (a.s) shi ne tabbatar da abin koyi na har abada wajen tsayar da gaskiya da adalci da kuma fada da zalunci.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Duk wanda ya kama tafarkin Imam Husain (a.s) wajibi ne ya yi shirin shahada, duk kuwa da cewa ba wajibi ne sakamakon hakan ya zamanto shi ne shahadar ba, to amma hakan lamari ne da ke tabbatar da sa'ada da kuma daukaka a koda yaushe.
Yayin da yake magana kan irin rikon da al'ummar Iran suka yi da wannan tafarki na Imam Husain, Jagoran cewa ya yi: Al'ummar Iran sun shigo cikin fage ne da ruhi irin na Ashura, don haka suka sami nasarar kawar da wani tsari na zalunci, sannan kuma a madadinsa suka kafa tsarin Musulunci.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Har ya zuwa yanzu dai al'ummar Iran sun ci gaba da riko da wannan tafarkin, sannan kuma dukkanin ci gaban da al'ummar Iran suka samu, sun same su ne albarkacin riko da wannan tafarkin.
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin falalar da ke cikin watan Sha'aban wanda ya bayyana shi a matsayin watan ibada da tawassuli da kuma neman kusaci da Allah Madaukakin Sarki, don haka ya yi kira da a karfafa abubuwan da suke kara kusata mutane da Ubangiji na daga addu'oi da sauransu musamman Munajat al-Sha'abaniyya da kuma neman gafara da rahamar Ubangiji.
A wani bangare na jawabin nasa kuma, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi karin haske kan zaben shugaban kasar da za a gudanar ranar 14 ga watan Yunin nan inda ya kirayi al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatansu wajen kada kuri'arsu don bada wa makiyansu kasa a ido.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Makiyan Musulunci, juyin juya halin Musulunci da kuma Iran sun tattaro dukkanin karfinsu na kudi da kafafen watsa labarai da na siyasa wajen raba al'ummar Iran da wannan tsari na Musulunci da kuma sanya su yin mummunan kallo da kuma zato ga hukumar da ke gudanar da wannan zaben, to amma da yardar Allah, a ranar Juma'ar nan mai zuwa (ranar zaben kenan) al'ummar Iran da dukkan karfinsu za su tabbatar wa da duniya irin karfafaffiyar alakar da ke tsakaninsu da wannan tsarin ta hanyar fitowar da za su yi kwansu da kwarkwatarsu, sannan kuma a wannan karon ma za su bada wa makiya kasa a ido da kuma kwance musu zani a kasuwa.
Har ila yau Jagoran ya gode wa ‘yan takaran shugabancin kasar da suke ta magana dangane da wajibcin girmama doka da kuma irin yadda al'umma suke ci gaba da girmama dokar a yayin yakin neman zabe sabanin abin da ya faru a lokacin zaben da ya gabata, kamar yadda kuma yace duk wani shugaban da za a zaba zai zamanto mai kare manufofin kasa da al'ummar Iran ne.
1241892