IQNA

Kasar Algeria Za ta Gudanar Da Wani Shiri Na Kyautata Rayuwar Jama'a

17:59 - June 24, 2013
Lambar Labari: 2551471
Bnagaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Algeria suna da shirin daukar matakai na tababtar da cewa an kyautata rayuwar jama'a a bangarori daban daban wanda hakan zai bas u damar ci gaba da rayuwarsu ba tare da matsanannciyar wahala ba.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, mahukuntan kasar Algeria suna da shirin daukar matakai na tababtar da cewa an kyautata rayuwar jama'a a bangarori daban daban wanda hakan zai bas u damar ci gaba da rayuwarsu ba tare da matsanannciyar wahala ba kamar yadda suka fuskanta aa baya ba.

A bangare guda kuma Hukumomi a yammacin kasar Algeria sun fidda wani sabon tsari na rarraba makamacin man fetur da gas ga ababen hawa a yankin don hana fasa korinsu zuwa kasar Morocco.
Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya nakalto AFP na kasar Faransa yana cewa tun kimani mako guda da ya gabata ne, hukumomi a jihar Tilmisan a yammacin kasar suka bullo da wani tsari na rarraba man fetur da gas ga ababen hawa bisa rabon da ko wani abin hawa ya ke da shi don tabbatar da cewa ba wanda zai sami damar kwasar man fetur ko gas daga kasar don fasa korinsa zuwa kasar Morocco.
Gwamnatin kasar Algeria dai tana bada tallafi ga makamacin man fetur da Gas ga masu ababen hawa a cikin kasar, amma ta gano cewa wasu mutanen suna sayen man fetur da gas da arha a cikin gida su kuma yi fasa korinsa zuwa kasar Morocco inda suka cika aljihunsu da riba mai yawa.
A wani labarin kuma bayan wannan matakin da gwamnan jihar Tilmisan ya dauka wasu mutane sun fito zanga zanga zuwa gidan gwamnan inda suke bukatar ya yi watsi da tsarin.
Matakin dai ya sanya an fara samun layin ababen hawa a gidajen mai na jihar, sanadiyyar bincike da ake gudanarwa kafin a sayarwa ko wani abin hawa makamashi.

1246842








captcha