Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka dai ana ci gaba da yin Allawadai da kakkausar murya a dukaknin kasashen musulmi dangane da kisan gillar da aka yi wa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Alah su tabbata agare shi akasar Masar da suka hada da daya daga cikin manyan malamai na kasar Sheikh Shehata.
An dai gudanar da Jana’izar mabiyar tafarkin mazhabar Ahlulbait da ‘yan kungiyar Salifiya suka kashe a kasar Masar. A marecen yau talata ne a gudanar da zana’izar Mutane nan mabiya tafarkin mazhabar Ahlulbait guda 4 da ‘yan kungiyar salafiya suka kaisu da shahada.
Janazar mutane 3 a masallacin Sayyidatun nafisa dake tsakiyar garin Alkahira wanda hakan ya kara kawo bacin ran al’umma ga kungiyar Salafiya a kasar sannan mutun guda an binne shine a garin Bahira dake arewacin kasar.
Rahotanni sun tababtar da cewa a ranar lahadi ne wasu ‘yan kungiyar salafiya suka kai hari a gidan Babban malamin nan Sheik Hasan Shuhata daya daga cikin shugabanin Shi’a a kasar Masar inda suka sameshi tare da dan uwansa da talibbansa guda biyu sannan suka kaisu da shahada.
Amma daga nata waje gwamnati ta bada sanarwar kama Mutane 8 wadanda ake zarkin su kan cewa sunada hannu wajen kashe wadannan bayun Allah dab a sub a su gani ba.
1248363