IQNA

Sojoji a kasar Masar sun baiwa ‘yan siyasar kasar awa 48 da su warware rikicin kasar

23:56 - July 01, 2013
Lambar Labari: 2554857
Bangaren kasa da kasa a dazu ne kakakin rundunar Masar Abdul fatah Sise a gidan talbijin na kasar ya bayyana cewa rundunar sojan kasar ta baiwa ‘yan siyasar kasar dama ta karshe na awa 48 da su tabbatar da muradin Al’ummar kasar. Idan bah aka ba to sojen kasar zasu dauki matakan da ya dace.

Kamafanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo cewa, dazu ne kakakin rundunar Masar Abdul fatah Sise a gidan talbijin na kasar ya bayyana cewa rundunar sojan kasar ta baiwa ‘yan siyasar kasar dama ta karshe na awa 48 da su tabbatar da muradin Al’ummar kasar. Idan bah aka ba to sojen kasar zasu dauki matakan da ya dace da bukatun al'umma.

Rundunar Sojan ta akkada cewa bata goyan bayan ko wani gungun ‘yan siyasa na kasar . a matsayinta na rundunar tsaro wajibe ne ta kare kasar da muradun ‘yan kasar.
Kakakin ya kara da cewa ci gaba da jinkiri na iya kawo karin zubar da jini a kasar

Wannan bayyanai na zuwa ne bayan da Ma’aikatar kiwan lafiya ta kasar ta bada labarin kashe Mutane 16 daga jiya zuwa yau a yayin da zanga-zangar ke shiga kwanakinta na biyu.

1250840







captcha