IQNA

Masu adawa da Morsi sun bukaci da ya gagagua safka daga kan mulki

23:53 - July 03, 2013
Lambar Labari: 2556182
Bangaren kasa da kasa, Dubun-dubutar magoya bayan shugaban kasar Masar da kuma masu adawa da shi ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Alkahira da ma wasu biranan kasar a jiya, inda lamarin da ya kai ga yin taho-mu-gama a wasu yankuna tsakanin bangarorin biyu, inda aka tabbatar da mutuwar mutane 3 da suka hada da wani ba'amurke, wasu da dama kuma suka samu raunuka. A birnin Alkahira dubban magoya bayan Mohammad Morsi sun taru ne a masallacin Rabi'at Adwiyyah.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, nda suka yi ta rera taken nuna goyon bayansu gare shi, tare da sukar masu adawa da shi, yayin da dubban masu adawa da Morsin kuma suka taru a dandalin Tahrir, wasu kuma suka taru a kofar fadar shugaban kasa da ke yankin Ittihadiyyaha cikin birnin na Alkahira, inda suke kira ga Morsi da ya gaggauta safka, domin abin da suka kira gazawarsa a dukkanin bangarori tun bayan da ya karbi shugabancin kasa shekara guda da ta gabata, tare da killace mukamai da dukakin harkokin gudanarwa a kasar ga 'yan kungiyar 'yan uawa musulmi kawai, sauran mutane kuma sun zama 'yan kallo, yayin da wasunsu kuma suke bayyana Morsi da kungiyar 'yan uwa musulmi a matsayin wadanda suka sace juyin juya halin da al'ummar kasar suka yi a kan gwamnatin Husni Mubarak, inda Morsi da kungiyarsa suka kafa wata gwamnatin da bata da bambanci da ta Husni Mubarak.

A birnin Iskandariya kuwa, dubban mutane ne suka kai farmaki kan ofishin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muhammad Morsi, inda suka banka masa wuta, biyo bayan wata taho mu gama da aka yi tsakanin 'yan kungiyar ta 'yan uwa musulmi da kuma masu adawa da Muhammad Morsi a garin na Iskandariya, babban jami'in 'yan sanda na birnin ya ce wani ba'amuke ya rasa a yayin gumurzun a lokacin da yake daukar hotuna, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta tabbatar da wannan labari, inda ta bukaci jami'an huldar diplomasiyyarta da ke kasar da ayyukansu ba su zama dole ba, da su bar kasar, kamar yadda ta bukaci Amurka da ke nufin yin tafiya zuwa Masar da su dakata.

Rikicin na Masar dai ya kara kamari ne biyo bayan jawabin da shugaban kasar Muhammad Morsi ya gabatar a Larabar da ta gabata, inda ya dora alhakin dukkanin abin da yake faruwa na tashe-tashen hankula a kasar a kan bangarorin siyasa da suke adawa da shi, inda ya kira da mabarnata, tare da shan alawashin shiga kafar wando guda da su, duk kuwa da cewa daga bisani a cikin bayaninsa nasa ya kiraye su zuwa ga tattaunawa, amma bangarorin adawar sun yi watsi da wannan tayi nasa, tare da bayyana hakan a matsayin wani shure-shure ne da Morsi ke yi, domin kuwa a cewarsu a gobe Lahadi za su gudanar da wata zanga-zanga mafi girma a kasar, wadda za ta kai ga kifar da gwamnatinsa, daga bayan gabatar da jawabin Morsia daren Laraba zuwa safiyar yau Asabar, mutane 7 ne suka rasa rayukansu, wasu fiye da 500 kuma suka samu raunuka sakamakon rikicin da ya biyo bayan jawabin nasa.

Ko shakka babu abin da yake faruwa a kasar ta Masar a halin yanzu ba bushara ce ta alkhari ga makomar kasar ba, musamman ma idan aka yi la'akari da yadda 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi da kuma wasu daga cikin 'yan salafiyya na kasar suka tsaya kai da fata tare da gindaya rayuwarsu a kan cewa ba za su taba amincewa da duk wani mulki in ban a Morsi ba, a daya bangaren kuma masu adawa da magoya bayansu suka tsaya kai da fata a kan cewa dole sai Morsi ya safka domin gudanar da wani zabe na gaggawa, kuma ga dukkanin alamu ba daya daga cikin bangarorin biyu da yake shirye domin yin sassuci kan matsayinsa.

1251511
captcha