IQNA

Babban Malamin Jami'ar Azahar ya yi Kira Da a Gudanar da Zabuka Ba Da Bata Lokaci ba

15:18 - July 06, 2013
Lambar Labari: 2556551
Bangaren kasa da kasa, bababn malamin jami'ar Azahar a kasar masar ya yi kira da a gudanar da zabuka ba tare da bata lokaci ba bayan kifar da gwamnatin Muhammad Morsi wanda hakan zai bayar da damar ci gaba da dimokradiyya a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Dr Ahmad tayyib bababn malamin jami'ar Azahar a kasar masar ya yi kira da a gudanar da zabuka ba tare da bata lokaci ba bayan kifar da gwamnatin Muhammad Morsi wanda hakan zai bayar da damar ci gaba da dimokradiyya a kasar wadda ke fama da matsalolin siyasa.
Shugaban jami’ar Al-Azhar Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana amincewarsa da matakin da aka daukan inda ya yi kira da a gudanar da zaben cikin gaggawa. Haka nan shi ma a nasa bangaren shugaban Cocin Kifdawa na kasar Paparoma Tawadros na 2 shi ma ya sanar da amincewarsa da matakin da aka daukan kamar yadda su ma ‘yan Salafiyya na kasar karkashin jam’iyyar Al-Nur suka sanar da amincewarsu saboda abin da suka kira kare zubar da jinin al’ummar Masar. Shi kuwa Muhammad Baradei, wakilin jam’iyyun adawa a wajen tattaunawa da sojojin, bayan bayyanar da amincewarsu da matakin da sojojin suka dauka, ya sanar da cewa taswirar hanyar da aka cimma za ta lamunce gudanar da ingantaccen zabe cikin gaggawa a kasar.
Shi kuwa tsigaggen shugaba Morsi ta shafinsa na facebook ya sanar da rashin amincewarsa da abin da ya kira juyin mulki inda ya kirayi magoya bayansa da su fito don fada da hakan cikin hanyar ruwan sanyi, kungiyar Ikhwanul Muslimin, wacce shugaba Morsin ya fito daga cikinta ta yi Allah wadai da abin da ta kira juyin mulkin wanda ta ce zai mai da kasar Masar zuwa ga lokacin mulkin zalunci da babakere.
Ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da inda tsohon shugaban yake ba, sai dai kuma wasu majiyoyi suna nuni da cewa sojojin suna ci gaba da rike shi tare da wasu manyan jami’an gwamnati, kamar yadda kuma suke ci gaba da farautar wasu daga cikin kusoshin kungiyar Ikhwanul Muslimin na kasar ta Masar.

1252399



captcha