Bangaren kasa da kasa, hanyoyin da suka dace domin duba watan Ramadan mai alfarma da ke shirin kamawa a cikin kwanaki biyu masu a kasashen musulmi da kuma abubuwan day a kamata akiyaye a wajen ganin watan na Ramadan kafin tabbatar da shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, hanyoyin da suka dace domin duba watan Ramadan mai alfarma da ke shirin kamawa a cikin kwanaki biyu masu a kasashen musulmi da kuma abubuwan day a kamata akiyaye a wajen ganin watan na Ramadan kafin tabbatar da shi a shar'ance.
A bangare guda a wani labari na daban shugaban kasar Tunusiya ya tsige babban malamin gwamnatin kasar da ke bada fatawa daga kan mukaminsa. Ofishin shugaban kasar Tunusiya a cikin daren jiya ya fitar da sanar cewa: Shugaban kasar Munsif Marzuki ya tsige Sheikh Usman Badikh daga kan mukaminsa na babban malamin gwamnati mai bada fatawa a kasar, inda ya maye gurbinsa da Sheikh Hamadah Sa'id.
Bayanin ofishin shugaban kasar ta Tunusiya bai fayyace dalilin daukan wannan mataki na tsige muftin kasar Sheikh Usman Badikh daga kan mukaminsa ba, sai dai wasu majiyoyi suna bayyana cewar sabani ne ya kunno kai tsakanin muftin Tunusiya Sheikh Usman Badikh da mahukuntan kasar kan bukatar da wasu malamai suka gabatar na shelanta jihadi kan kasar Siriya amma muftin kasar Sheikh Usman ya ki amincewa da bukatarsu da ta yi daidai da na mahukuntan Tunusiya karkashin jagorancin jam'iyyar Annahadha ta masu ra'ayin Islama.
1253702