IQNA

Masu akidar kafirta musulmi su ne abbabr matsala ga musulmi a duniya

0:02 - July 08, 2013
Lambar Labari: 2557830
Bangaren kasa da kasa, masu akidar anna ta kafirta al'ummar musulmi su ne babbar matsala ahalin yanzu ga musulmi a duniya baki musamman ma bayan matakan da tsohon shugaban Masar ya dauka na taimaka musu kai tsaye.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labarin na daban shugaban rikon kwarya na kasar Masar Adli Mahmud Mansur ya sanar da rusa majalisar dokokin kasar ta Masar, wadda akasarin mambobinta 'yan kungiyar 'yan uwa musuolmi ne tare da abokan kawancensu na kungiyar salafiyyah.

Wannan bayan sanar da rusa majalisar dokokin ta Masar, Adli Mansur ya sanar da nada Muhammad Ahmad Farid a matsayin sabon shugaban hukumar leken asiri kuma mai ba shi shawar akn harkokin tsaro, tare dasafke Muhammad Rif'at da Morsi ya nada kan wannan mukami a kwanakin baya.

Kasashen duniya na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta dangane da tumbuke Morsi daga kan karagar shugabancin Masar, inda Amurka ta nuna damuwa matuka kan lamarin, tare da dakatar da taimakon da take bayarwa ga Masar har sai ta ga abin hali ya yi nan gaba, yayin da sauran kasashen turai suke kira da a gaggauta komawa ga tsarin dimokradiyya ta hanyar shirya zabuka ba tare da bata lokaci ba.

Sojojin dai sun kifar da Morsi ne bayan samun amincewar jami'ar Azahar da babbar majami'ar kasar gami da akasarin bangarorin siyasa da suka hada hard a jam'iyyar Nur ta 'yan salafiyyah, bayan tabbatyarc da cewa akasarin mutanen kasar ba su amince da ci gaban shugabancinsa ba.

1253655




captcha