IQNA

An kai hari a birnin Beirut na kasar Lebanon da nufin haifar da fitina

23:57 - July 09, 2013
Lambar Labari: 2559136
Bangaren kasa da kasa, an kai harin ta'addanci a cikin birnin Beirut an kasar Lebanon da nufi haifar dafitina tsakanin al'ummar kasar ad suke da kyakkayawar alaka da gwagwarmayar muslunci karkashin jagoran ungiyar hzibullah ta hanayar yin amfani da masu akidar kafit=rta musulmi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, an kai harin ta'addanci a cikin birnin Beirut an kasar Lebanon da nufi haifar dafitina tsakanin al'ummar kasar ad suke da kyakkayawar alaka da gwagwarmayar muslunci karkashin jagoran ungiyar hzibullah ta hanayar yin amfani da masu akidar kafitrta musulmi duniya baki daya.

Tarwatsewar wata mota da aka makare da bama bamai a yankin kudancin kasar Labanon ta jikkata mutane akalla 38 tare da janyo hasarar dukiyoyi. A safiyar yau Talata wata mota da aka cika da bama bamai ta tarwatse a wajen ajiyar motoci da ke yankin Bi'ir Abdi a kudancin kasar Labanon lamarin da ya janyo jikkatan mutane akalla 38 tare da konewar motoci masu tarin yawa. Shaidun ganin ido sun bayyana cewar bayan tarwatsewar motar hayaki bakinkirin ya mamaye sararin samaniyar yankin, kuma harin ta'addancin ya yi sanadiyyar lalata gidajen fararen hula da suke yankin.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya ko jama'a da suka dauki alhakin kai harin, duk da cewar rikicin kasar Siriya ya yi mummunar tasiri a cikin kasar Labanon sakamakon rabuwan kai da aka samu tsakanin al'ummar Labanon, inda wasu ke goyon bayan ayyukan ta'addancin da ake gudanarwa a kasar ta Siriya domin kifar da gwamnatin kasar yayin da wasu ke goyon bayan gwamnatin ta Siriya.

1255367





captcha