IQNA

An Gudanar Da Taron Karatun Alkur'ani Mai Girma A Gidan Jagora Imam Khamenei

10:17 - July 13, 2013
Lambar Labari: 2560234
A ranar farko ta watan Ramalana mai albarka, watan saukar Alkur'ani mai girma, ne aka gudanar da majalisin karatun Alkur'ani mai girma na tsawon sa'oi uku da rabi a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yayin wannan taron wanda taron wanda ya sami halartarJagoran juyin juya halin Musuluncin, malamai, makaranta da mahaddata Alkur'ani mai girma sun karanto wasu ayoyi na Alkur'anin. Har ila yau kuma wasu matasa sun rera wasu wakoki na yabon watan Ramalana mai albarka.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron, Jagoran juyin juyin juya halin Musuluncin Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana tilawa, tajwidi da haddar Alkur'ani a matsayin share fagen samar da al'ummar Akur'ani da ake fatan kafawa yana mai cewa: A cikin al'umma ta Musulunci wajibi ne a yi riko da koyarwa ta Alkur'ani datsarin rayuwa ta Musulunci.

Ayatullah Khamenei ya bayyana karatu da haddar Alkur'ani a matsayin share fagen fahimtar Alkur'ani da misaltuwa da halaye da dabi'un Alkur'ani. Jagoran yaci gaba da cewa: wajibi ne al'adun al'umma ta Musulunci su zamanto sun yi daidai da kyawawan halaye na Alku'ani da koyarwar Ma'asumai (amincin Allah ya tabbata a gare su).

Har ila yau yayin da yake ishara da kokarin da wasu suke yi na lalata al'adu da tsarin rayuwa da alaka ta zamantakewa ta al'umma, Jagoran yayi ishara da al'adun kasashen yammaci yana mai cewa: koyin da mafi yawa daga cikin al'ummomin duniya suke yi da al'adun kasashen yammaci ba dalili da hujja ba ce wajen aiki da irin wadannan al'adun a cikin al'ummar musulmi ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Wajibi ne koyarwarAlkur'ani mai girma ta zamanto ita ce abin koyi a cikin al'umma musulma.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Addini, lafiyayyen hankali da kuma maganganun Ma'asumai (amincin Allah ya tabbata a gare su) su ne koyarwar Alkur'ani mai girma da wajibi ne a yi riko da kuma koyi da su cikin al'umma ta Musulunci.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya nuna farin cikinsa dangane da yadda matasa suke komawa da kuma nuna so da kaunarsu ga Alkur'ani mai girma, tilawarsa da kuma haddarsa yana mai cewa: Wajibi ne dukkanin al'ummar su kulla alakarsu da Alkur'ani, don kuwa karatu da kuma fahimtar Alkur'ani wani matakin farko da kuma share fage ne na yin tunani cikinsa.


1256471
captcha