Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ana ci gaba da samun rahotanni da suke nuni da cewa har yanzu ana samun masu nuna tsananin kiyayya ga mabiya addinin musluncio a kasar faransa musamman ma mata masu saka hijabin musulunci a kasar inda har ma ake kai hari a kansu.
A wani labarin kuma Fira ministan kasar Libiya ya jaddada cewar a karkashin sabon tsarin tsaron kasa da zai bullo da shi babu wanda ke da hakkin rike makami sai jami'an tsaron kasar, shafin internet na Al-Youm As-Sabi a yau Alhamis ya watsa rahoton cewa: Fira ministan kasar Libiya Ali Zaidan ya jaddada cewar a karkashin sabon tsarin gudanar da tsaron kasa da zai bullo da shi da nufin tsarkake birnin Tripoli fadar mulkin kasar daga makamai, babu wanda ke da izinin rike makami sai jami'an tsaron kasar kawai wato sojoji da 'yan sanda.
Har ila yau Ali Zaidan ya fayyace cewar nan da wasu 'yan kwanaki zai sanar da sunan sabon ministan tsaron kasar Libiya, kuma kasashen Amurka, Faransa, Birtaniya da Italiya ne zasu dauki alhakin horas da sabbin dakarun soji da na 'yan sanda da yawansu ya kai 1500 da za a dauka aiki a tsakanin kungiyoyin 'yan bindigan kasar da suka yi yakin a lokacin neman hambarar da gwamnatin kama karya ta Mu'ammar Gaddafi, kuma za a horas da sune a wajen kasar Libiya.
1258318