IQNA

Limamin juma'a a Tehran ya bayyana damuwa dangane da halin da ake iciki a kasar Masar

23:58 - July 19, 2013
Lambar Labari: 2563612
Bangaren kasa da kasa, wanda ya jagoranci Sallar Juma’a anan birnin Tehran ya bayyana damuwa akan halin da kasar Masar ta ke ciki a halin yanzu bayan kifar da Morsi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatullah Ahamd Jannaty ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da su ka jefa masar a mawuyancin halin da ta ke ciki, shi ne matakin da Muhammadu Mursi ya dauka wanda bai dace ba akan h.k. Isra’ila.

Limamin juma’ar na Tehran ya kara da cewa; Rufe mashigar Rafah da gwamnatin Muhammadu Mursi ta yi da ci gaba da riko da yarjejeniyar Camp-David da ci gaba da aikewa h.k. Isra’ila iskar gas da kuma alakar diplomasiyya mai karfi a tsakaninsu, abubuwa ne da su ka sabawa manufofin juyin al’ummar wannan kasa.

Limamin na Tehran ya bayyana fatansa na ganin al’ummar Masar sun ci gaba da kare hadin kansu su kuma kawo karshen zubar da jinni da fadace-fadace a tsakaninsu.

Ayatullah Ahamd Jannaty ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da su ka jefa masar a mawuyancin halin da ta ke ciki, shi ne matakin da Muhammadu Mursi ya dauka wanda bai dace ba akan haramtacciyar kasar yahudawa.

1260268










captcha