Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wannan firici na zuwa bayan wani hari baya bayan da aka kai a guraren ajiyar Motoci na Masalacin Isa bn Suleiman inda wata Mota shake da bama-bamai ta tarwatse a wannan guri.inda Gwamnati ke zargin ‘yan adawa da hanu wajen kai wannan hari.
Shugaban Maluman ya kara da cewa Gwamnati ta kama ‘yan adawar kasar da dama wanda suka hada da manyan maluma,’yan siyasa,likitoci da manyan masana shara’a sanan tuhumar da Gwamnati ke musu zarki ne marassa tushe.
Al’umma za ta ci gaba da nemen ‘yan cinta ta hanyar ruwan sanhi kamar gudanar da zanga-zanga har sai taga ta cimma bukatunta.
Al’ummar Bahrain sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin ransu kan wani samame da Jami’an tsaron kasar suka kai a gidan babban malamin nan Dan shi’a Sheik Isa Kasim.
A jiya juma’a da safe Jami’an tsaron suka kai samame a gidan Babban malamin nan Dan Shi’a Sheik Isa Kassim, a yayin da suka je gidansa basu samu babban malamin a gida amma sun kuble iyalansa cikin wani daki inda su kayi gaggaran bincike a gidan sannan sun ba ta abubuwa da dama a gidan
A kwanakin baya ma Gwamnati tayi barazanar kashe wannan babban malamin.
Al’ummar kasar Bahrai taja kunnan Gwamnati da kadda ta sake irin wannan cin mutunci ga wannan babban malami inda tace duk abinda ya samu wannan malami to alhakinsa na wuyan Gwamnatin.
1266133