Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban jam'iyyar Annahdha ta masu ra'ayin Islama da ke mulki a kasar Tunusiya Rashid Ghannusi ya yi furuci da cewar gwamnatocin kama karya ne ake rusa su ta hanyar gudanar da zanga-zanga da matsin lambar 'yan adawa, ba gwamnatocin da aka zaba ta hanyar dimokaradiyya ba, don haka matsin lambar 'yan adawar Tunusiya ba zai taba yin tasiri wajen kawo karshen halartacciyar gwamnatin kasar ba.
Ghannushi ya kuma yi kakkausar suka kan kiraye-kirayen da ake yi na neman rusa zababbiyar gwamnatin Tunusiya da aka kafa bayan samun nasarar juyin juya halin kasar. Ghannushi ya kara da cewar a kowane zamani ana iya samun matsala ko bullar masifa, amma ba ta hanyar rusa gwamnati ba ce kadai za a kai ga magance matsalar.
Kanfanin dillacin labarai na kasar Faransa ya habarta cewa Ministan cikin gidan kasar Tunisia Lutfi Bn Jadwi a yau talata ya bayyana cewa daga watan Maris zuwa wannan wata na Augusta da muke ciki kimanin Matasa 'yan tawaye dubu 5 ne jami'an tsaron kasar suka samu nasarar hanawa zuwa kasar Siriya don taimakawa 'yan ta'addar kasar. Har ila yau jami'an tsaro sun kama wasu Matasa guda 50 wadanda suke kokarin zuwa kasar ta siriya don hadewa da 'yan ta'adda
.Jaridar Ashuruk wadda ake bukata a kasar Tunisia ta habarta cewa daga tsakiyar watan Maris da ya gabata zuwa yanzu kungiyar dake safarar Matasan tunusia zuwa kasar Siriya don yin jihadi a fadarsu na samun dallar Amurku dubu uku.
1269750