IQNA

Imam Khamenei : Imam Khamenei : Yaki A Kasar Syria Zai Shafi Dukkan Yankin

13:50 - August 29, 2013
Lambar Labari: 2582041
Bnagaren siyasa, Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Aya. Sayyed Aliyul Khaminaee ya bayyana cewa duk wani yaki wanda kasar Amurka zata soma a kasar Syria zai shafi yankin gaba daya ne, zai kuma taba bukatun ita Amurka a cikinsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran ya bayyana haka ne a jiya laraba a lokacinda yake ganawa da shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani tare da majalisar ministocinsa a nan Tehran. Jagoran ya kara da cewa Amurka zata yi asara kwatankwacin wanda ta yi a kasashen Iraqi da Afganistan.
Shi yaki a cikin wasu kasashe, inji shi zai haifar da rikici ne ya kuma haifar da kiyayya ga wadanda suka yi shishigi, a wani bangare na jawabinsa dangane da kasar Masar kuma, jagoran ya ce ba ya nufin shiga cikin lamuran wata kasa, amma kuma ba zai runtsa idanunsa kan kisan kiyashin da akewa mutanen kasar ba. Muna Al..wadai da kisan mutanen kasar Masar wadanda basa dauke da makami.
Daga karshe jagoran ya bukaci a maida tsarin democradia a kasar Masar, tare da zaban shuwagabanni kasar kamar yadda aka saba a irin wannan tsarin.
Ya ce a lokacin da yakejawabi a jiya laraba a lokacinda yake ganawa da shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani tare da majalisar ministocinsa a nan Tehran. Jagoran ya kara da cewa Amurka zata yi asara kwatankwacin wanda ta yi a wasu kasashen.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa daya daga cikin lamurra masu tsananin hatsari da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiyan shi ne shigo da addini, bangaranci da kuma mazhaba cikin sabani na siyasa da ake da shi a wadannan kasashe yana mai cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa wasu kasashen yankin nan sun taimaka wajen kafa wata kungiya ta masu kafirta musulmi wadanda suke fada da dukkanin kungiyoyin musulmi. To amma wajibi ne masu goyon bayan wannan kungiya (mai kafirta musulmi) su san cewa wannan wutar da suka kunna su ma ba za ta barsu ba.
Har ila yau Jagoran ya bayyana haramtacciyar kasar Israila a matsayin babbar barazana ta koda yaushe ga wannan yankin wacce kuma take samun goyon bayan Amurka ido rufe, don haka sai yace: Lalatacciyar gwamnatin sahyoniyawa wacce ta mallaki rumbunan makaman kare dangi masu hatsarin gaske tana a matsayin gagarumar barazana ce ga yankin nan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: yankin nan yana bukatar tsaro na gaba daya. Ba za a iya cimma wannan manufa mai muhimmanci ba kuwa in ba ta hanyar kawo karshen makaman kare dangi a yankin nan ba.

1279701
captcha