IQNA

Hambararren Shugaba Mursi Zai Gurfana Gaban Kuliya A Cikin Wata Nuwamba

12:07 - October 13, 2013
Lambar Labari: 2603151
Bangaren kasa da kasa, kafofin yada labarun gwamnatin Masar sun rawaito cewa a ranar 4 ga watan Nuwamba wanan shekara ne hambararren shugaban kasar Mohammed Mursi zai gurfana gaban kotu. Za a gurfanar da tsohon shugaban ne tare da wasu mutane 14 a gaban kuliya bisa tuhumarsu da hannu a mutuwar masu zanga-zanga da dama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ana tuhumar tsohon shugaban na Masar da hannu a mutuwar masu zanga-zanga a lokacin wani bore a gaban fadar shugaban a cikin watan Disamban shekarar 2012. A cikin watan Yuli da ya gabata ne sojojin suka kifar da gwamnatin Mursi na kungiyar 'Yan uwa Musulmi, tun locacin ne kuma ake tsare da shi a wani wuri da ba sani ba. Su kuma magoya bayan kungiar ta 'Yan uwa Musulmi sun yi ta gudanar da zanga-zangar neman a sake maido da shi kan karagar mulki.
Wani dan kunar bakin wake ya kashe sojojin Kasar Masar hudu a yankin Sina da ke kan iyaka da Palasdinu a yau alhamis. Majiyar Soja ta bayyana cewa dan kunar bakin waken da ya ke cikin wata mota mai makare da bama-bamai ya kutsa cikin wani shinge na gudanar da bincike da ke kan hanyar birnin al-Arish, inda ya tarwatsa kansa a tsakanin sojoji tare da kashe hudu daga cikinsu nan take. Wannan dai shi ne hari na biyar da aka kai wa sojojin Masar a cikin kwanaki hudu da su ka gabata a wannan yankin.
A jiya laraba ma dai an kai wa jami’an tsaro da su ke gadin gidan Rediyon yankin na Sina hari ta hanayr harba musu makaman roka daga kan gine-ginen da su ke kusa. Tun bayan kifar da gwamnayin shugaba Muhammad Mursi ne dai yankin na Sina ya ke fuskantar kai hare-hare daga kungiyoyin da su ke dauke da makamai.
1302166



captcha