IQNA

Yan ta’adda sun kai harin bam a yau a kasar Syria

22:51 - October 25, 2013
Lambar Labari: 2608107
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Syria sun ce wasu mutane da ake zaton ‘yan ta’addan kasar ne sun kai hari da wata mota da suka shakare da bama-bamai a yammacin yau a kusa da wani masallaci da ke yankin Wadi Burdi a kusa da birnin Damascus.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin din kasar Syria ta ce ‘yan ta’adda na kungiyar Jabhat-Nusra ne da suke da alaka da kungiyar Akaida suka kai harin da bama-bamai masu karfin gaske, kuma sun kai harin ne a kusa da wani masallaci da ke yankin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula tare da jikkatar wasu, sai har yanzu ba iya samun bayani dangane da adadin mutanen da suka rasa rayukansu a wannan hari ba.
A wani bangaren kuma rahotanni sun tabbatar da cewa a yau sojojin an Syria sun samu narasa kashe mayakan kungiyar ta Jabhat-Nusra fiye da 40 a kusa da birnin Lazakiya, da suka hada da wasu manyan jagororin kungiyar ‘yan kasar Saudiyya, da kuma wasu daga kasar Jordan.
Rakin kudaden aiyukan Soja da kasar ta Amurka ta yi na iya sanya jami'an tsaron Amurka su janye daga cibiyar tsaro ta nahiyar Afirka dake kasar Italiya wato Africom, kokarin da wasu manyan janar na Sojan Amurka ke yin a dauke cibiyar tsaron ta Afirka zuwa wani kasa a nahiyar Afirka bai samu nasara ba.
A halin yanzu kasar ta Amurka ta sake meka wannan bukata na cire cibiyar tsaro daga kasar Italiya zuwa wata kasar Afirka saboda harin da aka kaiwa wannan cibiya.
Ko da yake suma sojojin na Amurka ba tsira su kai a kasashen na afirka,a shekara ta 1993 Sojojin Amurka sun kwashi kashinsu a hannu daga mayakan kungiyar Ashabab, harin baya-bayan nan wato na 5 ga watan Octoba da Komdodin Amurka suka kai a sansanin kungiyar Ashabab shi ke nuna cewa har yanzu jami'an tsaron Amurka ba su dauki izina ba kan abinda ya faru da su a shekarun baya.





captcha