IQNA

Shugaban Iran Ya Bukaci A Yi Bincike Cikin Kisan Jami'an Tsaron Kan Iyakar Kasar

23:25 - October 27, 2013
Lambar Labari: 2609171
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhadi ya bada umurni ga ma’aikatar cikin gida da kuma Bangaren siyasa, ma’aikatar harkokin wajen kasar gabatar da binciken da ya dace don gano dalilan da suka jawo shahadar jami’an tsaron kan iyakar kasar 17 a kan iyakar kasar da kasar Pakistan a daren jumma’an da ta gabata.Ruhani ya gabatar da ta’aziyarsa ga iyalan jami’an tsaron da suka yi shahada, da kuma ga jagoran juyin juya halin Musulunci Aya. Sayyeed aliyul Khaminiaee.
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya ce, Dr Ruhani ya bukaci ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kammala shirye shiryen kulla yerjejeniyar tsaro tare da kasar Pakistan don magance matsalolin tsaron da ke faruwa a kan iyakokin kasashen biyu daga lokaci zuwa lokaci, a musayar wutan da ya auku tsakanin jami’an tsaron kan iyaka na kasar Iran da kuma wasu yan bindiga a garin Sarawan a yankin sistan Buluchistan a daren jumma’an da ta gabata, jami’an tsaro 17 suka yi shahada a yayinda wasu 6 suka ji rauni.

A wani labarin kuma Shugaban kasar Iran sheikh Hassan Rauhani ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da yin iyakacin kokarinta domin ganin an kai ga warware rikicin da aka haddasa a kasar Syria ta hanyar lumana.

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Syria Lakhdar Ibrahimi a birnin Tehran, inda ya ce akasarin kasashen da suke ta tasiri kan rikicin Syria yanzu sun kai matsayar cewa babu maita illa tattaunawa da warware rikicin ta hanyar lumana, wanda kuma a cewarsa shi ne matsayin tun farko, ya kara da cewa Iran za ta bayar da dukkanin hadin kai domin ganin taron Geneva kan kasar Syria ya kai ga nasara.

A nasa bangaren Lakhdar Ibrahimi ya bayyana cewa Iran tana da babbar tasiri a kan duk wani batu na kawo karshen rikicin da ake fama da shi a Sria, a kan ya ce halartar Iran a taron Geneva ya zama wajibi, ya kuma yaba da irin bayanan da ya ji daga jami’an gwamnatin kasar dangane da shirinsu na halartar taron.

1308292
captcha