Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a Makun da ya gabata ‘yan sanda a birnin Munbasa sun kai wani mumunan farmaki a wasu masalatai wadanda suka hada da masalatan Musa,Sakina, Mina da Safa sannan suka yi awan gaba da dariruwan Masallata da wannan Masalatai zan karkin yin zagon kasa ga tsoron kasa.
Har ila yau jami’an ‘yan sandar sun yi dawa’ar cewa sun kama makamai a cikin wadanda masallatai, zarkin da musulmin na kasar suka musanta.
Shugabanin musulmin a kasar sun nuna rashin amincewar su da take-taken Gwamnatin na cin zarafin Al’ummar musulmi a kasar ta Kenya da nufin yaki da ta’addanci.
A bangare guda ‘yan majalisun kasar ta Kenya sun bayyana damuwarsu da wannan mataki inda suka ce rufe masalatan da aka yi ba kan ka’ida ne ba, sannan sun bukaci Gwamnati da tagaggata kawo karshen wannan mataki.
'yan ta'adda da ke dauke da akidar kafirta musulmi suna yin amfani da masallatai wajen yada akidarsu da kuma ajiye makamai, kamar dai yadda jami'an tsaro a kasar suka tabbatar tare da nuna hotunan wuraren da aka kai hari tare da samunsu.
2611327