Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, fitaccen dan siyasa a kasar Masar kuma shugaban jam’iyyar congress Jamal Hanafi Taha ya bayyana abin da wasu ‘yan siyasa masu fakewa da addini suke yi na daga kur’ani a lokacin gangami ko wani rikici tsakaninsu da jami’an tsaro da cewa wannan lamari ne na yaudara da bata sunan addinin muslunci.
Wannan furuci ya zo sakamakon abin da wasu daga cikin magoya bayan kungiyar ‘yan musulmi suke yi ne a lokacin da suke zanga-zanga ko wani gangami a kasar sukan daga kur’ani, wanda kuma hakan ya tabbata a tarihin muslunci cewa wadanda suka fara yin wannan abu mayaudara ne, kuma sun rudi wasu wawaye daga cikin muslumi, wanda hakan ya zama babban abin da ya kawo rarraba tsakanin musulmi a lokacion da ake kokarin murkushe wadanda suke kokarin bata sunan musulunci.
Jamal Hanafi Taha ya ci gaba da cewa wasu yan siyasa sun mayar da sauran mutane musulmi tamkar wawaye, domin kuwa a lokacin da mutum ke bukatar bayyana matsayinsa babu bukatar ya yi yaudara da kur’ani, domin kuwa dukkanin maganar da ake yi ta siyasa ce da neman mulki da matsayi, ko da mutum ya yi amfani da sunan addini wajen kamfe, to bai dace kuma kur’ani ya zama a bin wasa da yaudara ta siyasa ba.
Da dama daga cikin malamai da masana akasar Masar dai suna sukar irin wannan mataki da mabiya kungiyar yan uwa musulmi suke dauka na yin amfani da kur’ani mai tsarki tare da daga shi a gaban jami’an tsaron Masar a lokacin zanga-zanga, wanda hakan kan kai ga tozarta matsayin wannan babban littafi mai tsarki, lamarin da malamai suka haramta shi.
2612005