IQNA

An kawo Karshen Gasar Hardar Kur’ani Da Tajwid A Garin Sabha Na Libya

23:58 - December 02, 2014
Lambar Labari: 2614536
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar hardar kur’ani mai tsarki a garin sabha da ke arewacin kasar Libya tare da halartar mahardata daga sassa na yankinkuma ‘a a sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar a mako mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwasat  cewa an kawo karshen gasar hardar kur’ani mai tsarki a garin sabha da ke arewacin kasar Libya tare da halartar mahardata daga sassa na yankinkuma ‘a a sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar a mako mai zuwa kamar dai yadda majiya ta tabbatar.
Tun kwanakin da suka gabata ne aka fara gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki da kyautata tajwidinsa a jami’ar Asmariyyah dake garin Sabha da ke kudancin kasar Libya da nufin karfafa daliban kur’ani mai tsarki a kasar.
Wannan bayani y ace bayanin ya ci gaba da cewa hardar za ta kunshi juzu daban-daban  haka nan kuma yan kasa da shekaru goma  za su yi harda ne kawai zuwa izihin tabarak, juzu’I na ashin da tara  kuwa zai kebanci yan kasa da shekaru sha biyu ne, kamar yadda juzu’I na 28 zai kebancinci yan shekara sha biyar, har zuwa ‘yan shekaru ashirin, kamar yadda juzui na ashirin da hudu  zai hada da bangarori daban-daban na shekaru na mahalarta.
Gasar  dai tana cikin muhimman ayyukan da wannan cibiyar ilimi ta fara aiwatarwa da nufin karfafa harkokin kur’ani mai tsarki a kasar, wadda a halin yanzu take fama da matsaloli na tsaro da tashin hankali, wanda ya hada yankunan kudanci da gabaci musamman, inda ake samun sauki lamurran a yankunan arewaci.
2614098

Abubuwan Da Ya Shafa: Sabah
captcha