IQNA

An Yi Allawadai Dangane Da Azabtar Da Fursunoni Da Hukumar CIA Ta Amurka Ke Yi

17:46 - December 10, 2014
Lambar Labari: 2617552
Bangaren kasa da kasa, majalisar musulmin kasar Amurka ta yi kakkausar suka dangane da rahoton da aka fitar da ke bayyana cewa hukumar CIA yana azabtar da fursunonin da ake tsare da su.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam-Online cewa, a jiya hadakar majalisar musulmin kasar Amurka ta yi kakkausar suka dangane da rahoton da aka fitar da ke bayyana cewa hukumar CIA yana azabtar da fursunonin da ake tsare da su a gidajen kaso a kasashe daban-daban.
Rahoto kwamitin binciken sirri a majalisar datijan Amurka yayi mumuna suka ne akan hanyoyin da hukumar leken assiri Amurka wato CIA ke amfani da su dan tatsar bayanai akan wadanda ake zargi da ayyukan ta'adanci dama iayalan su.   Hanyoyin wadanda aka bayana su da wuce kima sun hada da galazalawa wandanda aka aka kama bisa zargi da ayyukan ta'addanci harma iyalansu ana musu barazana.  
Hanyoyin mafi muni dai sun hada da tsare wadanda ake zargin na tsawan shekaru suna fuskantar tambayoyi ta munanen hanyoyi na kuntatawa fiyeda kima na tsawan kwananki harma zuwa makonni.   Rahoto ya ce ana bankare wadanda ake zargin tumbir kan bango, ana kuma tsoma su cikin ruwan sanyi masu kankara, ana kuma hana su barci har na tsawan mako guda, ko baya ga hakan rahoto ya ce ana masu munanan duka tareda barazana, ana kuma kaskanta su da dai sauran ababe mafi muni da suka keta hakokin bil adama kamar yadda rahoto ya walafa bayan binciken daya aiwatar a cikin wasu bayanan siri da offishin ministan shari'a Amurka tsakanin .
Mafi muni dai a cewar rahoto na majalisar datijan Amurka shine na yadda hukumar ta CIA take hanawa wadanda ake zargin barci na kimanin sa'O'I 180 kwatamcin rashin kwana na mako guda da kwana daya, ko kuma rataya kai kasa kafafu sama.   Sanata Dianne Feinstein wace  ta jagoranci wannan kwamitin binciken ta ce rahoton ya yi nazari kan yadda hukumar leken asiri Amurkar wato CIA ta yi amfani da wannan hanya mai cike da gallazawa wajen neman bayanai ga wasu mutane 6000.   
A hannun daya dai  Shugaban wanan kasa  ya bayyana hanyar da jami'an leken asiri na (CIA) ke bi wajen tatsar bayanai da cewa hanya ce mai haifar da rudani, tareda firta cewa hanyar ''bama kawai zubar da kimar kasar ta Amirka ba a idon duniya tun daga satumban 2001, hakan ya sanya basa samun hadin kai kan muradun su da kawayensu cikin sauki.   shugaban ya bayyana haka ne bayan da kwamitin binciken sirri a majalisar dokokin kasar da aka bawa alhakin gudanar da wannan aiki kan cibiyar ya fitar da rahotan na jiyya Talata.  
Wanan dai ya kara zubarda mutuncin na Amurka a idon Duniya, tareda jefa 'ya 'yan ta dake ketare cikin hadari, bayan irin tofin alla-tsine da kasar ta sha a 'yan kwanakin nan na kin hukuntan 'yan sanda nan fara fata da suka ashe bakaken fata nan cikin harda karamin yaro.
2617257

Abubuwan Da Ya Shafa: CIA
captcha