IQNA

Mujallar Kasar Faransa Ta Sake Buga Zanen Batunci Ga Manzon Allah

10:54 - January 15, 2015
Lambar Labari: 2710785
Bangaren kasa da kasa, mujallar Charlie Hebdo ta kasar faransa a yau Laraba ta sake buga zanen batunci ga manzon Allah (SAW)

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar CNN cewa, mujallar Charlie Hebdo ta kasar faransa a yau Laraba ta sake buga zanen batunci ga manzon Allah (SAW) duk kuwa da irin bacin rai da musulmi suka nuna kan hakan.
Wannan mujalla an buga kwafi miliyan 3 a cikin yaruka 6, haka nan kuma wasu jaridu da mujallu da nashrori kimanin 60 sun buga ta, yanzu haka dai al’ummar musulmi a kasashe daban-daban suna ci gaba da yin Allah wadai da tofin Allah tsine ga mujallar nan ta kasar Faransa ta Charlie Hebdo saboda zanen batanci ga Annabi Muhammadu (s.a.w.a) da ta buga a jiya Laraba kamar yadda kuma suke Allah wadai da halin ko in kula da kasashen yammaci suke nunawa. 
Ita ma a nata bangaren kungiyar gwagwarmayar musulunci cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Laraban ta yi Allah wadai da wannan zanen batancin wanda ya sosa ran sama da musulmi biliyan daya da rabi na duniya tana mai cewa irin wannan batancin ne yana taimakawa yaduwar ayyukan ta’addanci da tsaurin ra’ayi.
Wasu kasashen ma an gudanar da gagarumar zanga-zanga don yin Allah wadai da wannan danyen aikin. Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun nufi ofishin jakadancin Faransa da ke kasar don nuna rashin amincewarsu da batancin da mujallar ta yi wa Manzon Allah (s.a.w.a).
A ranar talata Babban mai bayar da fatawa a Masar Shaughi Allam ya bayyana wannan lamari da cewa babban cin zarafi ne ga dukkanin al’ummar musulmi na duniya baki daya, kuma duk abin da yake faruwa kan masu aikata hakan su ne suka ja ma kansu.
2707422

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha