IQNA

Daesh Ba Su Da Wata Alaka Da Addinin Musulunci

20:14 - February 13, 2015
Lambar Labari: 2846213
Bangaren kasa da kasa, Babban mai bayar da fatawa a kasar Masar Sheikh Shuki Allam ya bayyana cewa 'yan ta'addan takfiriyya masu kafirta musulmi abin da suke aikatawa ba shi da wata alaka da addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na AlAhram cewa, a cikin wani bayaninsa babban mai bayar da fatawa a kasar Masar a bayyana cewa 'yan ta'addan takfiriyya masu kafirta musulmi abin da suke aikatawa ba shi da wata alaka da addinin muslunci, balantana koyarwarsa mai tsarki.

A wata fatawa da ya fitar a yau Juma'a, babban malami mai bayar da fatawa na kasar Masar Sheikh Shuki Allam ya ce, kungiyoyin Takfiriyyah Alkaida da dangoginta da suka hada da ISIS da sauransu, dukkanin abin da suke yi da sunan jihadi ko kafa daular muslunci ba shi da wata alaka da muslunci.

Shehin malamin ya ce abin ban takaici ne yadda ake yin amfani da matasa da ba su da wata masaniya dangan eda addinin muslunci, kuma ake anke kwakwalensu da wasu muggan akidu na kafirta musulmi tare da kai ma musulmi hare da kasshe ta hanyar yi masa yankan rago ko kone duk da sunan jihadi a tafarkin sunnar manzon Allah (SAW)

Ya ce wannan bala'i da ya sami al'ummar musumi, kuma hakki ne a kan kowane musulmi ya yaki wannan mummunar akida da dukkanin abin da zai iya, musamman ma malamai masu kyakyawan saiti kan addini.

2844145

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha