Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, cibiyar Azahar ta addinin muslunci a kasar Masar ta mayar da martini da kakkauasar murya tare da yin Allawadai da kisan da aka yi wa kibdawa misrawa 21 a Libya ta hanyar yankan rago da ‘yan ta’addan ISIS suka yi musu.
Bayanin na Azhar ya ce kisan Misrawa 21 ta hanyar yankan rago da ISIS suka yi a Libya da cewa aiki ne na dabbanci, wanda mutum mai imani da lamiri na 'yan adamtaka ba zai iya aikata shi ba, balanatan har wadannan dabbobi su danganta kansu da addinin mulunci ko sunnar ma’aiki mai tsira da amincin Allah da iyalan gidansa tsarkaka.
A nata bangaren rundunar sojin Masar ta ce jiragen kasar sun kaddamar da hare-hare da jijjifin safiyar yau a kan sansanonin mayakan kungiyar 'yan ta'adda na ISIS a cikin kasar Libya, bayan da kungiyar da cewa ta kashe wasu Kibdawan Masar 21 a kasar ta Libya.
Rundunar sojin kasar Masar ce ta sanar da hakana cikin wani bayani da ta fitar a safiyar yau Litinin, inda ta ce harin ya nufi sansanonin 'yan ta'addan ISIS da kuma wasu runbun ada suke ajiye makamai, kuma a cewar bayanin dukkanin hare-haren an kaddamar da su a cikin nasara.
.
A jiya ne kungiyar ta ISIS da ke da'awar jihadi ta fitar da wani faifan bidiyo, wanda a cikinsa ta nuna yadda 'ya'yan kungiyar suka yi wa kibdawan Masar 21 yankan rago, lamarin da ke ci gaba da fuskantar kakkausar suka da Allah-wadai daga kasashen duniya.
A jiya ne ‘yan ta’addan an ISIS suka fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda suka kashe kibdawan ‘yan kasar Masar su 21 da suke gudanar da su a cikin kasar ta Libya inda suka yi musu yankan rago da wuka, tare da shan alwashin ci gaba da aikata irin wanann danyen aiki a kan mabiya addinin kirista.