IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki A Najeriya

23:50 - March 24, 2015
Lambar Labari: 3036057
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki a jahar Sokoto dake yamma maso arewacin Najeriya a cikin watanni biyu masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Daily Trust cewa, bangaren da ke kula da harkokin addinin muslunci a jami’ar Dan Fodio da ke birnin na Sokoto ne zai dauki nauyin shirya da kuma gudanar da wannan gasa.
Ja’afar kaura wanda shi ne shugaban kwamitin da ke daukar nauyin shirya irin wadannan taruka na gasa, ya bayyana wa wannan kafar yada labarai cewa, babbar manufar shirya wannan gasa dai ita ce kara yada koyarwar kur’ani mai tsarki a tsakanin al’ummar musulmi na Najeriya.
Ya kara da cewa an shirya gudanar da gasar ne a cikin wannan wata, to amma saboda yanayi na zabuka da za a gudanar a kasar, hakan ya sanya ala tilas aka dage zuwa watanni biyu a nan gaba, a lokacin komai ya lafa.
Najeriya dai ita ce kasa mafi girma  adukkanin nahiyar Afirka wadda kuma tafi yawan jama’a, wadanda mafi yawansu mabiya addinin muslunci ne, sai kuma mabiya addinin kirista da ke wasu bangarori na kasar.
3030989

Abubuwan Da Ya Shafa: Sokoto
captcha