Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, a yau an gudanar da zaman sauraren shari'ar babban sakataren jam'iyyar adaw ta Alwifaq a Bahrain Shekh Ali Ali Salman a karo na uku a babbar kotun kolin kasar.
Mahukuntan kasar ta Bahrain sun dauki matakin hana dukkanin jami'ai daga jam'iyyar adawa ta Alwifaq shiga dakin shari'ar, a zaman na yau kotun ta yi ta maimaita zarge-zarge da tuhuna ta karya kan sheikh Ali Salman, lamarin day a kore, kum aya jadda cewa ba zai taba ja da baya ba dangane da gwagwarmayar da yake yi domin tabbatar da cewa al'ummar kasar sun rayu cikin 'yanci da karama.
A nasu bangaren mutanen Bahrain suna gudanar da wata gaggarumar zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da shari'ar zalunci a kan shugaban jam'iyyar ta wifaq Sheikh Ali Salamn tare da neman a saki dukkanin fursunonin siyasa da ake tsare da su a kasar bisa zaluncin mahukunta.
Mahukuntan na Bahrain dai sun kame Sheikh Ali Salman tun ranar 28 da takwas ga watan disamban shekara da ta gabata, bisa hujjar cewa za su gudanar da bincike ne a kansa, amma tun daga lokacin suka saka a gidan kaso suna masu tuhumarsa da cewa yana kokarin kifar da masarautar kasar ta Bahrain.
Ya zo a cikin wani bayani da kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar kan wannan lamari a jiya, sun bayyana cewa dukkanin abin da masarutar Bahrain ke tuhumar Sheikh Ali Salman da shi kage ne na siyasa, kuma haka baya rasa nasaba da yunkurin da gidan sarautar kasar ke yi na murkushe mabiya mazhabar shi’a wadanda su ne kashi tamanin da shida na al’ummar kasar Bahrain, tare da nisantar da su daga duk wani sha’ani na siyasa ko tafiyar da mulki a kasar.
Yanzu haka dai akwai lauyoyi kimanin hamsin da takwas na kasa da kasa da suka dauki nauyin bin kadun wanann shari'a tare da kare wanda ake tuhuma a gaban kotu.
3040118