IQNA

Ammar Hakim Ya Ce Za A Tsarkake Yankin Anbar Baki Daya Daga Daesh

23:48 - May 19, 2015
Lambar Labari: 3305569
Bangaren kasa da kasa, shugaban majalisar koli ta muslunci a Iraki Sayyid Ammar hakim ya bayyana cewa za a tsarkake yankin Anbar baki daya daga yan ta’addan Daesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Hamrain News cewa, Sayyid Ammar Hakim shugaban majalisar koli ta muslunci a Iraki a yayin ganawa da jakadan kasar Turkiya ya bayyana cewa za a tsarkake yankin Anbar baki daya daga yan ta’addan Daesh masu kisan jama’a.
Shi ma a nasa bangaren fira ministan kasar Iraki ya musanta labarin cewa ‘yan kungiyar ta’addanci ta Da’ish sun kwace iko da dukkanin garin Ramadi fadar mulkin lardin Anbar.
A jawabinsa ga al’ummar Iraki a jiya Juma’a ya bayyana cewar a cikin wasu ‘yan sa’o’i gaskiya zata bayyana domin nasarar jami’an tsaron Iraki da suke samun tallafin dakarun sa-kai zata fito fili, kuma ‘yan ta’adda zasu kwashi kashinsu a hannu.

 

Rahotonni da suke fitowa daga garin na ramadi suna bayyana cewar jami’an tsaron Iraki sun yi luguden wuta kan ‘yan ta’addan Da’ish da suka mamaye majalisar shawarar garin na amadi lamarin da ya tilasta musu janyewa daga wasu yankunan garin.

3305492

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha