IQNA

Yaki Da Daesh Wajibi Ne Na Shari'a Ta Addini

23:56 - June 02, 2015
Lambar Labari: 3310740
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Kahalid Mulla ya bayyana cewa yaki da kungiyar ta'addanci ta Daesh wajibi ne na shari'ar addini.


Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ittijah Press cewa, Sheikh Khalid Mulla wanda shi ne shuagaban kungiyar malamai a kudancin Iraki ya bayyana cewa yaki da Daesh dole ne domin kuwa suna bata sunan muslunci.

Malamin ya ci gaba da cewa wanann kungiya tana yin amfani da sunan muslunci wajen yin dukaknin ayyuka na barna da kuma zubar da jinin bil adama duk da sunan suna kare wannan addini ko kuma tabbatar da shi, wanda hakan ya bakanta sunan addinin muslunci a idon duniya.

Ya ci gaba da cewa aiki ne da ya rataya kan malamai da kuma sauran wadanda suke da hankali daga cikin musllmi ko suke da fada aji da su amfani da dama da sukeda ita wajen takawa wadanddan dabbobin mutane birki, tare da bayyana ma duniya cewa abin da suke yi bas hi ne muslunci ba.

Dangane da kuma masu daure musu gindi da kuma basu fatwa, ya bayyana cewa dukkanin aikin su daya, masu yin hakan ma sun fi muni, domin kuwa Daeshe mahaukata ne jahilai da ba su san addini a, amma wanda ya sanya su kan wannan mummunar hanya ya fi muni a kansu.

Y ace dole n al'ummar Iraki su zama cikin fadaka kada s yarda da rudu da sunan bangarenci su zama suna goyon bayan ta'addanci, y ace wannan ba shi ne ba, ya kirayi jama'a baki aya su zama cikin tunani da fadaka.

3310353

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha