IQNA

Yan Ta’adan Daesh Sun Mayar da Hubbaren Annabi Yunus (AS) Wurin Wasanni

23:49 - June 20, 2015
Lambar Labari: 3316534
Bnagaren kasa da kasa, yan ta’addan Daesh sun mayar da makabartar annabi Yunus (AS) wurin wasanni domin tozartar alfarmar wurin da ma’abocinsa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumariyyah News cewa, yan ta’addan Daesh sun mayar da makabartar annabi Yunus (AS) wurin wasanni ba tare da masu basu fatawa sun komai kan lamarin ba.

Yan ta'addan kungiyar ISIL sun yanka limamin masallacin Annabi Yunus (AS) da ke birnin Mausil a arewacin kasar Iraki, bayan da yaki ya mika musu masallacin, da kuma kin bayar da fatawar korar kiristoci daga birnin.

Daya daga cikin shugabannin kabilun larabawa 'yan sunna a  garin Mausil Sheikh Barham Al-ta'i ya bayyana wa tashar talabijin ta Al-Iraqiyah a daren jiya cewa, 'yan ta'addan na ISIL sun bukaci sheikh Abdulsalam da ya mika musu masallacin Annabi Yunus (AS), kuma ya bayar da fatawar haramcin barin kiristoci a cikin garin na Mausil, inda ya sheda musu cewa ba zai yi hakan ba, a nan take suka yanka shi.

A nasu bangaren sojojin kasar Iraki suna ci gaba da nausawa a cikin yankunan da 'yan ta'addan suka kwace iko da su, inda suke ci gaba da fatattakarsu, domin dawo da doka da oda a yankunan, da kuma dawo da dubban daruruwan mutanen da 'yan ta'addan suka kora daga yankunansu.

3316343

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha