Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, Zayid Shaker daya daga cikin jagororin maiya addinin muslunci a kasar ta Amurka ya bayyana cewa, yanzu haka musulmi a kasar ta Amurka sun fara gudanar da gangami na hada kudade domin sake gina majami’oin mabiya addinin kirista n na kasar mallakin bakken fata da aka kona da wuta.
Ya ci gaba da cewa akwai majamiu guda 7 da aka kona dukkaninsu na mabiya addinin kirista bakaken fata ne, kuma za su gyara su domin nuna raham da jin kai irin na addinin muslunci ga dukkanin ‘yan adam.
A cikin yan lokutan da suka gabata an kai hare-hare a majamiu na mabiya addinin kirista a sassa daban-daban na Amurka musamamn a Chalston, inda aka kona tare da kasha adadi mai yawa na bakaen fata a cikin majamiu.
Musulmin sun bayyana cewa za su yi hakan domin kara tabbatar wa Amurkawa cewa addinin sun a zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da saurana addinai, da kuma jin kai ga dukkanin bil adama, wanda kuma hakan shi ne hakikanin koyarwa ta addinin muslunci.
A mahangar addinin muslunci babu wani banbanci tsakanin mutane ko fararare ne ko bakake, dukkaninsu ‘yan adam ne bayin Allah madaukakin sarki.
3326129