Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Inter Az-a cewa, Muhammad Nujaimi mamba akwamitin kungiyar kasashen musulmi ya bayyana cewa akwai kure a cikin sanarwar da aka bayar a wasu kasashe dangane da ganin watan sallah, da hakan ya hada har da kasar Saudiyya, kuma ita kasar ta amince da hakan.
Ya ce ya zama wajibi a kan al’ummar kasar da suka sha azumi bisa sanarwar da aka bayar da su rama azumi guda daya bayan salla kuma su ciyar, domin hakan shi ne matsayin kaffara ta azumin da suka sha na wannan shekara.
Dangane da wannan kure y ace ko shakka babu hakan tana faruwa, kuma sau da yawa sai hakan ya faru ne ake ganewa daga bisani, amma tun da shari’a ta tanadi hukunci, sai ayi amfani da shi daidai da yadda ta yi umarni.
Ya ce wannan bas hi ne karo na farko da aka samu hakan ba, kuma ba zai zaman a karshe ba, domin kuwa matkar ana rayuwa to kuwa ba za aiya kauce ma kure ba, sai dai kawai lamari ne da ke bukatar taka tsatsan matuka akowane lokaci.
Haka nan shi ma Shekh Hamdah Said babban mai bayar da fatawa akasar Tunisia ya bayyana cewa, yana neman uzuri saboda irin wannan kure da aka samu a kasar.
3331472